
Dakarun Sojin saman Najeriya (NAF) na musamman a yau, 12 ga watan Janairu, 2022, sun ceto mutane 26 da aka yi garkuwa da su a yayin da suke sintiri a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.
Aikin ceton ya faru ne a lokacin da dakarun na musamman suka ci karo da wasu motoci guda 5 babu kowa a cikin su kuma kofofin su a bude a Anguwar Yako, lamarin da ke nuni da cewa mutanen ciki an sace su ne da kuma yiwuwar yin garkuwa da su.
Dakarun,sun fara gano wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su sun fito kwatsam daga cikin jeji. Bayan bincike mai zurfi a cikin yankin, an ceto jimillar mutane 26 da abin ya shafa.

Da ake yi wa wadanda abin ya shafa tambayoyi daga Birnin Gwari zuwa wurare daban-daban da suka hada da Kaduna, Minna da Kano, sun bayyana cewa, a yayin da suke cikin tafiya, sai ga wasu gungun ‘yan bindiga da dama da suka fito daga cikin jeji daga wurare daban-daban da ke kan hanyar, suka kewaye motocinsu.
Duk da namijin kokarin da rundunar ta yi, maharan sun gudu da wasu mutanen cikin daji.

Rundunar sojin saman, ta tsawaita ayyukan ta a yankin tare da fatan ceto sauran wadanda aka yi garkuwa da su yayin da aka kai wadanda aka ceto zuwa Asibitin sojojin smam na Kaduna domin duba lafiyarsu.


