
LOKACIN TSAFI DA SASSAN JIKIN MUTANE YAZO
Kasancewar siyasa ta karato, zaku ga ritual killings a fadin tarayyar Nigeria zai karu, wato a kashe mutane a cire sassan jikinsu domin ayi tsafi, wasu daga cikin miyagun ‘yan siyasa suna aikata hakan saboda neman kujeran mulki
Wannan matashin da kuke gani a hoto, ‘yan sanda sun kamashi a garin Jos, ya yaudari budurwansa ya kawota gidansa ya kashe ta, ya cire mata ido da farjinta.
Sannn a jihar Zamfara ma, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara ya fitar da sanarwa cewa sun kama wasu gungun mutane da suke sarrafa naman sassan jikin mutane suna sayar wa mayu da matsafa
Kaaruwai suna saurin fadawa tarkon matsafa masu sarrafa naman mutane, hakanan ‘yan mata masu kwadayi su ma suna saurin fadawa tarkon matsafa ba da kuma kananan yara wadanda basu mallaki hankalin kansu ba
Kananan yara a kula da su sosai, ayi musu huduba a tsoratar dasu kar su yadda wani mutum ya kirasu zuwa cikin lungu ko yace zai aikesu su amince, yanzu ba irin da bane, a fadakar da yara
Muna rokon Allah Ya karemu gaba daya
