Har Yanzu Ana Nemanta:

Hanifah

Har Yanzu Ana Nemanta: Kwanaki 40 Da Sace Hanifa A Birnin Kano

Yau kimanin kwanaki Arba’in (40) da wasu masu garkuwa da mutane su ka sace wata yarinya mai shekara biyar a birnin Kano.

Mutanen sun ɗauke Hanifa Abubakar ne da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a unguwar Kawaji bayan sun isa wurin a cikin babur mai ƙafa uku ko kuma Adaidaita-Sahu.

Wani kawun Hanifa ya shaida wa manema labarai cewa mutanen sun sace ta ne jim kaɗan bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya tare da sauran yaran maƙota.

Wasu daga cikin yaran da suka ga lokacin da abin ya faru sun ce “ɓarayin sun zo ne a Adaidaita-Sahu kuma suka ce za su kai su gida. Bayan sun kai su, sai suka ce Hanifa ta sake hawa don su ɗana ta, amma sai suka gudu da ita.”

Birnin Kano ya sha fuskantar sace-sacen ƙananan yara a ƴan shekarun nan, abin da ya sa Gwamna Abdullahi Ganduje ya kafa kwamatin bincike domin ganowa da kuma bin haƙƙin yaran da ake sacewa.

A Oktoban 2019, rundunar ‘yan sandan Kano ta kama wasu da ake zargin sacewa da kuma safarar yara ‘yan asalin jihar zuwa garin Onitsha na Jihar Anambra da ke kudancin ƙasar, inda ake tilasta musu sauya addini da al’ada.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started