EFCC ta kama Janar din karya, yace an nada shi shugaban rundunar sojin Najeriya

EFCC ta kama Janar din karya, yace an nada shi shugaban rundunar sojin Najeriya

Jami’an ofishin hukumar hana cin hanci da tashawa da yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC a Lagos, sun damke wani mai suna Bolarinwa Oluwasegun.

Oluwasegun yayi karyar shi hafsan soja ne mai mukamin Janar, wanda kuma shugaban kasa ya bada sunansa don nada shi babban hafsan sojan kasa na Najeriya.

Yayi amfani da wannan karya ne don damfarar da ta kai kimanin Naira miliyan 270.

Haka kuma wanda ake zargin, ya gabatar da takardar bogi mai dauke da da sa hannun shugaban kasa don yin damfarar tasa.

Acewarsa zai yi amfani da kudin ne don tabbatar da an nada shi wancan mukami na babban hafsan sojin kasa.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started